Kwararren Mai dafa abinci kuma shugaban wani gidan cin abinci a kasar Japan,Alan Fisher, ya goge tarihin kwararriyar Mai dafa abinci ‘yar Najeriya, Hilda Baci, wadda ita ce ta rike kambun wadda tafi kowa dadewa a tseren dafa abinci.
Fisher ya yi ikirarin shi ne mafi dadewa a tseren dafa abinci mafi dadewa bayan ya shafe sa’o’i 119 da mintuna 57.
Hakan ya nuna cewa Fisher ya zarta adadin lokacin da Hilda Baci ta shafe tana dafa abinci da sa’o’i 24.
Alan ya kuma yi da’awar tseren yin burodi mafi dadewa da ya shafe sa’o’i 47 da mintuna 21.
A baya dai Wendy Sandner Dan kasar Amurka ne ya rike kambun inda ya shafe sa’o’i 31 da mintuna 16.
Abin mamakin shi ne Alan ya shafe sama da sa’o’i 160 yana aikin girki a cikin dakin dafa abinci sama da sa’o’i 160 tare da hutun kwana kawai tsakanin sa’o’i 119 da minti 57 din farko da kuma sa’o’i 47 da mintuna 21 na biyu.