‘Yan bindiga sun kara kai hari yankin Sayaya dake karamar hukumar Matazu a jihar Katsina, tare da a kalla mutum biyar.
Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Talata, sa’o’I 24 bayan da suka kai wani harin lokacin taron Mauludi har suka hallaka mutum 25.
Mafiya yawan mutanen da aka hallaka a harin da ‘yan bindigar suka kai yayin taron Mauludin sun fito ne daga kananan hukumumomin Matazu da Musawa dake makwabtaka da juna.
Wani da yace mahaifinsa na daga cikin wadanda suka rasa rayukansu yayin harin, ya shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun shiga gida-gida ne inda suka hallaka mutum biyar tare da yin awon gaba da wasu da dama.
Yace ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu shanu tare da sace kayayyakin amfanin yau da kullum.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, mai Magana da yawun rundunar ‘Yan sandan jihar ta Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu, yace tun a ranar litinin din da ta gabata ne wasu gungun ‘yan bindiga suka farmaki kauyen Sayaya tare da yin harbe-harben kan mai uwa da wabi.