Da ɗumi-ɗumi :Jirgin sama ya yi hatsari a filin jirgin saman Kano

BREAKING 750x430

Wani jirgin sama mai zaman kansa da kamfanin sufurin jiragen sama na Flybird ke sarrafawa ya sauka cikin hatsari da safiyar Lahadi a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa jirgin, wanda ke ɗauke da fasinjoji 11 ciki har da ma’aikatan jirgi uku, ya sauka cikin hatsari da misalin ƙarfe 9:30 na safe bayan ya taso daga Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa an samu nasarar fitar da dukkan fasinjojin daga cikin jirgin ba tare da rahoton rasa rai ba a lokacin aukuwar lamarin.

Wani shaida da amarin ya faru a idonsa ya tabbatar da cewa an kwashe fasinjojin cikin gaggawa tare da tabbatar da tsaro a wajen da hatsarin ya faru.

Har yanzu dai ba a fitar da cikakken bayani kan musabbabin saukar jirgin cikin hatsarin ba, yayin da hukumomi ke ci gaba da tattara bayanai domin gano abin da ya haddasa lamarin.

Ana sa ran ƙarin bayani daga hukumomin da abin ya shafa yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here