Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC ta bayyana cewa Abubakar Malami, tsohon Antoni janar na tarayya, har yanzu bai cika sharuɗɗan belin da aka gindaya masa ba.
Hukumar ta yi wannan bayani ne a matsayin martani ga ikirarin Malami cewa an soke belinsa ne saboda halartarsa wani taron siyasa a jihar Kebbi, inda EFCC ta bayyana wannan ikirari a matsayin mara inganci.
Ana binciken Malami bisa zargin aikata laifuka 18 da suka haɗa da wanke kuɗi, amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba da kuma tallafa wa ta’addanci.
A wani bayani da mataimakinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai ya fitar, an yi ikirarin cewa Malami bai karya ko watsi da wani sharadi na belin da aka ba shi ba, sai dai EFCC ta musanta hakan gaba ɗaya.
Labari mai alaƙa: ADC ta zargi EFCC da siyasantar da soke belin Abubakar Malami
Hukumar ta bayyana cewa belin gudanarwa na wucin gadi ne da ake bayarwa bisa sharudda kafin kammala bincike da gurfanarwa a kotu, inda ta ce bayan yi masa tambayoyi an gindaya masa sharuɗɗa biyar da bai cika ko nuna shirin cikawa ba.
EFCC ta ƙara da cewa Malami ya nemi a ba shi rangwame kan halartar bincike bisa dalilin rashin lafiya, kuma duk da haka hukumar ta amince da buƙatarsa cikin tausayi duk da cewa bai gabatar da rahoton likita ko sahihin hujja ba.
Hukumar ta jaddada cewa ta sake gayyatar Malami domin ci gaba da bincike, kuma an tsare shi ne har sai ya cika sharuɗɗan belin da ya amince da su, tana mai cewa zargin soke beli da kuma hana shi harkokin siyasa ko tattaunawa da kafafen yaɗa labarai ba su da tushe, tare da ƙarfafa shi da ya mayar da hankali kan haɗin kai da masu bincike maimakon yada ikirarin da ba su da tushe a kafafen watsa labarai.










































