Jam’iyyar ADC ta soki EFCC bisa matakin da ta ɗauka na soke belin da aka ba tsohon Antoni janar kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami, inda ta bayyana hakan a matsayin siyasa ta bangaranci maimakon aiwatar da doka.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar a Abuja, inda ta ce hujjojin da ke akwai sun nuna cewa Malami bai karya duk wani sharadi da aka ɗora masa a belin ba, tare da jaddada cewa matakin bai da hujjar doka.
Bolaji Abdullahi ya yi gargaɗi cewa soke belin bayan da aka ruwaito Malami ya halarci wani taron siyasa a jihar Kebbi ya haifar da fahimtar cewa EFCC ta ɗauki matakin ne domin dakile burinsa na tsayawa takarar gwamna.
Duk da cewa jam’iyyar ta sake jaddada goyon bayanta ga EFCC da sauran hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa, ta yi gargaɗin cewa bincike na zaɓaɓɓe ko amfani da hukumomi wajen kai hari ga ’yan adawa na iya raunana amincewar jama’a ga yaƙin da ake yi da cin hanci da rashawa a Nijeriya.
Karanta: CITAD ta buƙaci a yi amfani da fasahar AI domin ƙarfafa Dimokuraɗiyya a Nijeriya
Jam’iyyar ta bayyana cewa Malami, wanda babban lauya ne na ƙasa, ya san wajibcin da ke tattare da beli, amma ba zai yi tsammanin cewa halartar tarukan siyasa zai zama hujjar soke belinsa ba duk da cikakken haɗin kai da ya bayar ga masu bincike.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa EFCC ba ta da ikon kundin tsarin mulki na dakatar da haƙƙin siyasa, inda ta yi gargaɗin cewa takaita motsinsa zuwa Kebbi kaɗai na nuni da yunƙurin gurgunta burinsa na siyasa, tare da neman a sake ba shi beli nan take.
NAN













































