Daraktan zartarwa na Cibiyar fasahar bayanai da ci gaban al’umma, Injiniya Y Z Ya’u, ya yi kira da a yi amfani da fasahar AI da fasahohin zamani ta hanyar da ta haɗa kowa domin zurfafa Dimokuraɗiyya da ƙarfafa tsarin mulki a Nijeriya.
Injiniya Ya’u ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Damaturu yayin gabatar da babban jawabi a taron ƙaddamar da gasar kirkire-kirkire ta Dr Kole Shettima kan Dimokuraɗiyya, wadda ƙungiyar Spotlight NG ta shirya.
Da yake jawabi kan taken taron da ya shafi amfani da fasahar AI wajen bunƙasa dimokuraɗiyya, ya bayyana cewa dole ne a tsara da aiwatar da fasaha ta hanyar da ke ƙarfafa shigar kowa da kowa da daidaiton shiga harkokin jama’a, ba tare da la’akari da ƙarfin jiki ko nakasa ba.
Ya nuna cewa fasahar zamani na taka muhimmiyar rawa a dimokuraɗiyya ta hanyar faɗaɗa ‘yancin faɗar albarkacin baki, samun bayanai da kuma shiga harkokin al’umma.
Ya ƙara da cewa kafafen yaɗa labarai na gargajiya da na sada zumunta sun buɗe hanyoyi ga ‘yan ƙasa su bayyana ra’ayoyinsu, su tattauna da shugabanni, su kalubalanci manufofi tare da shiga muhawarar jama’a.
Ya jaddada cewa ta hanyar kafafen yaɗa labarai da na sada zumunta, ‘yan ƙasa na iya isar da ra’ayoyinsu kai tsaye ga shugabanni tare da ɗora musu alhaki, sannan fasaha ta faɗaɗa ‘yancin taro ta hanyar mayar da shi zuwa sararin tattaunawa.
Injiniya Ya’u ya bayyana wayar da kai, samuwar kayan aiki, tsarin ɗora alhaki a matsayin ginshiƙai huɗu da ake buƙata domin amfani da fasaha yadda ya dace wajen ci gaban dimokuraɗiyya, inda ya yi bayanin cewa dole ne ‘yan ƙasa su san haƙƙoƙinsu na fasahar zamani, su samu kayan aiki, a kare su ta tsarin da ke ɗora alhaki, sannan farashin fasaha ya kasance mai sauƙi ba tare da ware kowa ba.
Ya kuma yi kira ga masu tsara manufofi, ƙungiyoyin farar hula da masu ƙirƙira fasaha da su fifita tsare-tsaren shugabanci na fasahar zamani masu haɗa kowa da ke ƙarfafa ƙimomin dimokuraɗiyya tare da tabbatar da cewa babu wani ɓangare na al’umma da aka bari a baya.
Har ma ya bayyana cewa gasar kirkire-kirkiren Dr Kole Shettima na da nufin gano, tallafawa da faɗaɗa ƙirƙire-ƙirƙiren matasa da ke bunƙasa dimokuraɗiyya, ɗora alhaki da shiga harkokin jama’a a Nijeriya da faɗin yammacin Afirka.













































