Tinubu zai sake fasalin cibiyar nazarin manufofi da dabarun ƙasa ta zama cibiyar ƙwarewa ta duniya – Shettima

IMG 20251213 WA0001 750x430

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta sake fasalin Cibiyar Nazarin Manufofi da Dabarun Ƙasa ta Nijeriya domin ta zama cibiyar ƙwarewa ta duniya mai amfani da fasahar zamani kuma mai ɗorewa wajen samar da kuɗi nan da shekarar 2030.

Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin da ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a bikin kammala karatun Manyan Darussan Gudanarwa na rukuni na 47 da aka gudanar a Kuru, a jihar Plateau, inda ya jaddada cewa shirin manyan darussan cibiyar wata gagarumar jarin gina shugabancin gaba ne ga ƙasar.

Ya bayyana cewa cibiyar, wuje ne da ake haɗa ra’ayoyi da ke tsara manufofi, jagorantar sauye-sauye, tare da tasiri ga tafiyar ci gaban ƙasa, yana mai nuna cewa wannan rawar ta sanya cibiyar zama ginshiƙi a harkokin tsare-tsaren ƙasa.

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta himmatu ƙwarai wajen tallafa wa cibiyar a shirin sauyinta, domin ta zama cibiyar ƙwarewa ta duniya mai tafiya da fasahar zamani, mai ƙarfi ta fuskar kuɗi, kuma wadda duniya ke girmamawa nan da shekarar 2030.

Karanta: Hajjin 2026: NAHCON ta buɗe shafin karɓar aikace-aikace domin haɗa tawagar likitoci ta ƙasa

Ya ƙara da cewa tallafin da gwamnati ke bai wa cibiyar bai tsaya kan kuɗi, gine-gine da yanayin bincike mai kyau kaɗai ba, sai dai yana tabbatar da cewa takardun manufofin da cibiyar ke fitarwa suna shirye don aiwatarwa tare da haɗa su kai tsaye cikin tsarin yanke shawara da aiwatarwa na ƙasa.

Shettima ya yaba da taken darasin Manyan Darussan Gudanarwa na rukuni na 47 kan tattalin arzikin teku da ci gaba mai ɗorewa a Nijeriya, inda ya ce, muhimmancin haɗa ci gaba, tsaro, kare muhalli da haɗin kan al’umma, tare da jaddada cewa ingancin binciken ilimi ya kamata ya kasance mai amfani a aikace kuma ya dace da halin da ƙasar ke ciki.

Ya tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu na ɗaukar tsara manufofi bisa hujjoji da muhimmanci, tare da bayar da umarnin ga ma’aikatun gwamnati, hukumomi da sassa daban-daban su yi nazari sosai kan rahotanni da shawarwarin waɗanda suka kammala karatun domin aiwatar da su nan take da kuma tsara tsare-tsaren dogon lokaci.

Shettima ya yaba wa darakta janar na cibiyar, Ayo Omotayo, da shugabanci da ma’aikata bisa jajircewa, yayin da gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang da shugaban kwamitin kula da cibiyar Ken Nnamani suka jaddada muhimmancin binciken cibiyar wajen magance ƙalubalen ƙasa.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here