Hajjin 2026: NAHCON ta buɗe shafin karɓar aikace-aikace domin haɗa tawagar likitoci ta ƙasa

NAHCON 1 2

Hukumar kula da aikin Hajji ta ƙasa NAHCON ta buɗe shafin karɓar aikace-aikace domin zaɓen mambobin tawagar likitoci ta ƙasa da za su gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.

An ƙaddamar da shafin karɓar aikace-aikacen ne a shafin hukumar na internet, domin bai wa kwararrun ma’aikatan lafiya damar gabatar da buƙatunsu ta hanyar tsarin da aka tanada.

Mataimakiyar daraktar yaɗa labarai da wallafe-wallafe ta hukumar, Fatima Sanda Usara, ta sanar da wannan mataki a cikin sanarwar da hukumar ta fitar.

Hukumar ta buɗe damar ga likitoci, masu hada magunguna, ma’aikatan jinya, da ma’aikatan kula da lafiyar muhalli da ke sha’awar shiga tawagar likitocin Hajji ta ƙasa, inda za su cike fom ɗin aikace-aikace ta shafin da aka ware.

Sanarwar ta bayyana cewa shafin karɓar aikace-aikacen zai buɗe daga ƙarfe 11 na dare zuwa ƙarfe 11 da minti 59 na daren ranar Litinin, tare da tanadin cewa masu nema dole ne su kasance suna aiki a halin yanzu a lokacin gabatar da aikace-aikacen.

Haka kuma, an shimfiɗa sharadin cewa duk mai neman aikin bai kamata ya taɓa shiga ayyukan Hajji na tawagar likitoci ta ƙasa a cikin shekaru ukun baya-bayan nan ba.

Hukumar ta ƙarfafa masu cika fom ɗin aikace-aikacen da su duba ƙa’idoji da buƙatun da aka gindaya a shafin hukumar a internet tare da cike bayanai yadda ya kamata, domin kauce wa cire su daga jerin masu cancanta, tare da miƙa buƙatunsu cikin lokacin da aka tanada.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here