Aƙalla fursunoni 12 ne suka tsere baya sun fasa wani gidan yari da ke garin Kotonkarfe a jihar Kogi.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ƙara da cewa tuni sun sake kama fursuna ɗaya daga cikin waɗanda suke tsere ɗin.
Karanta: Fubara ya musanta alaka da tsageru masu fasa bututun mai
Gwamnatin Kogi ta ce za ta haɗa ƙarfi da ƙarfe da jami’an tsaro domin gano yadda fursunonin suka samu nasarar tserewa a safiyar ranar Litinin.
Kwamishinan ya bayyana lamarin da abin takaici, “sannan yadda fursunonin suka iya tserewa ba tare da barin wata alama ba abin tambaya ne. Dole a gudanar da bincike mai zurfi, sannan a kamo fursunonin da suka tsere, sannan a gano waɗanda suke da hannu,” in ji Fanwo.