Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan fasa gidan yarin da aka yi na Koton Karfe da ke jihar Kogi.
Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Babatunde Alao ya fitar ranar Litinin a Abuja, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Ya sha alwashin tabbatar da cewa an kama duk fursunonin da suka tsere.
Labari mai alaƙa: Fursunoni 12 sun tsere daga gidan yari a jihar Kogi
Ministan ya kuma umurci mukaddashin Kwanturolan Hukumar Kula da gidajen yari na kasa Sylvester Ndidi Nwakuche, da ya ziyarci cibiyar da ke jihar Kogi domin tantance halin da ake ciki tare da fara bincike mai zurfi domin gano abubuwan da suka haddasa faruwar lamarin.
An samu labarin fasa gidan yari a gidan yarin a ranar Litinin, inda aka ce fursunoni 12 sun tsere, yayin da aka ce wani jami’in gidan yari ya bata.












































