Fubara ya musanta alaka da tsageru masu fasa bututun mai

Siminalayi Fubara 1

Gwamnan jihar Rivers da aka dakatar, Siminalaya Fubara ya musanta zargin da ake yaɗawa cewa yana da alaƙa da ƙungiyoyin ƴanbindiga da ke fasa bututun mai, inda ya ce hotuna da bidiyo da ake yaɗawa ƙarya ne.

Ya ce ana yaɗa labaran na ƙaryar ne domin a tayar da zaune tsaye a jihar, sannan a ɓata masa suna.

Fubara ya bayyana haka ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaransa, Nelson Chukwudi ya fitar, inda ya ce Fubara na Allah wadai da yada labaran na farfaganda.

Karin karatu: A karon farko Fubara ya fara fitowa cikin jama’a bayan dakatar da shi

“Gwamna Fubara ba shi da wata alaƙa da ƙungiyoyin ƴanbindiga masu fasa bututun mai, kuma bai taɓa tunanin ƙulla wata alaƙa da su ba, sannan kuma ba zai taɓa alaƙa da ɓatagari da suke barazana ga zaman lafiya da tattalin arzikin jihar Rivers ba,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Fubara ya nanata shirinsa na tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa, inda ya ƙara da cewa ba a cin moriyar gwamnati ba tare da zaman lafiya ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here