Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Taminu Turaki, ya bayyana cewa jam’iyyar ta shirya tsaf domin lashe zaɓukan gwamna na cike gurbi da ke tafe a jihohin Osun da Ekiti.
Turai ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa ta sirri da tsohon Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo a ɗakin karatunsa na shugaban ƙasa da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Turaki ya bayyana cewa PDP na da ƙuduri fiye da kowane lokaci na dawo da matsayinta a siyasar Nijeriya, yana mai girmama Obasanjo da sauran jagororin da suka kafa jam’iyyar bisa gudunmawar da suka bayar wajen gina dimokuraɗiyya da kyakkyawan shugabanci a ƙasar.
A ziyarar, Turaki ya samu rakiyar tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma Shugaban Kwamitin Amintattu na PDP Adolphus Wabara, tsohon Gwamnan Jihar Niger Muazu Babangida Aliyu, tsohon Gwamnan Jihar Plateau Jonah Jang, tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Oyo Taofeek Arapaja, da Shugaban PDP na Jihar Ogun Abayomi Tella, tare da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar.
Turaki ya bayyana cewa sun ziyarci Obasanjo ne domin gode masa kan hangen nesa da rawar da ya taka wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya da gina ƙaƙƙarfan hukumomi da ƙasar ke ci gaba da amfana da su.
Ya ƙara da cewa sun nemi shawarwari da jagoranci daga gare shi domin fuskantar manyan ƙalubalen da ke gaban jam’iyyar a tafiyarta ta gaba.
Karanta: Yanzu -yanzu: APC ta fitar da ɗan takarar gwamna a Osun
Ya yi amfani da karin magana wajen nuna muhimmancin koyon darasi daga gogaggun mutane, yana mai cewa ziyarar ta ƙara musu fahimta da ƙarfin guiwa.
Ya jaddada cewa duk da wahalar da ke gaban PDP, shawarwarin da suka samu sun shirya jam’iyyar domin tafiya nesa da kuma dawo da ita kan madafun iko nan gaba.
Turaki ya bayyana cewa PDP ta shiga yanayin shirye-shiryen yaƙin zaɓe na 2027, inda ya ce matakin farko shi ne kwato Ekiti sannan Osun.
Turai ya nuna cewa idan aka samu nasara a waɗannan jihohi biyu, babu wanda zai yi shakka cewa PDP na dawowa da ƙarfi domin ƙalubalantar gwamnatin APC.
A nasa jawabin, Shugaban PDP na Jihar Ogun Abayomi Tella ya bayyana ziyarar a matsayin sabon shafi ga jam’iyyar, tare da cewa mambobi sun samu sabon fata da ƙwarin gwiwa.
Ya jaddada cewa jama’ar jihar sun gaji da halin da ake ciki, kuma PDP ta shirya tsaf domin fafatawa da samun nasara a zaɓen da ke tafe.













































