Yanzu -yanzu: APC ta fitar da ɗan takarar gwamna a Osun

images 1 8 608x430

Tsohon shugaban Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Ƙasa a Nijeriya NIWA, Bola Oyebamiji, ya zama ɗan takarar APC a zaɓen gwamnan jihar Osun da za a yi a shekara mai zuwa.

An tabbatar da shi a matsayin ɗan takara bayan wakilai 1,660 suka amince da shi a taron fidda gwani na jam’iyyar.

Oyebamiji ya samu amincewa ne bayan ɗaya daga cikin masu neman takarar, Kunle Adegoke SAN, ya miƙa sunansa, yayin da wani ɗan takara kuma Sanata Babajide Omoworare ya mara masa baya.

Bayan haka, an kaɗa ƙuri’a ta murya inda dukkan wakilai suka amince da zaɓensa ba tare da wata adawa ba.

Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani, Gwamna Monday Okpebholo, ya ayyana Oyebamiji a matsayin ɗan takarar jam’iyyar bisa ikon da aka ba shi.

Ya bayyana cewa nasarar APC a zaɓen gwamna na shekarar 2026 za ta samu ne ta hanyar haɗin kai, tare da kira ga sauran masu neman takarar su yi aiki tare da Oyebamiji domin nasarar jam’iyyar.

Karanta: Soludo na kan gaba yayin da hukumar Zaɓe INEC ke sanar da sakamakon zaɓen gwamnan Anambra

Okpebholo ya ƙara da cewa bai taɓa shan kaye a zaɓe ba, yana mai jaddada cewa a matsayinsa na shugaban kwamitin zaɓe, APC za ta yi nasara a jihar.

Ya kuma yi kira ga masu zaɓe da su goyi bayan ɗan takarar da zai kawo ci gaba ga jihar, yana mai nuna cewa al’umma sun gaji da rawar siyasa mara amfani.

A jawabin karɓar nasara, Oyebamiji ya gode wa sauran masu neman takarar bisa janye burinsu tare da mara masa baya.

Ya danganta fitowarsa a matsayin ɗan takara da goyon bayan shugabanni da dattawan APC a matakin jiha da na ƙasa, sannan ya gode wa Shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa jagoranci da haɗin kan da ya samar a cikin jam’iyyar.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa manyan mutane sun halarci zaɓen fidda gwani, ciki har da Gwamnan jihar Ondo Lucky Aiyedatiwa, Gwamnan jihar Nasarawa Suleiman Abdullahi, da tsohon Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello.

Sauran sun haɗa da Ministan Harkokin Teku da Tattalin Arziƙin ruwa Gboyega Oyetola, Sakataren APC na ƙasa Surajudeen Basiru, shugabannin jam’iyya, da jami’an Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here