Soludo na kan gaba yayin da hukumar Zaɓe INEC ke sanar da sakamakon zaɓen gwamnan Anambra

Charles Soludo

Ɗan takarar jam’iyyar (APGA), Chukwuma Charles Soludo, na kan gaba a sakamakon zaɓen gwamnan jihar Anambra da aka gudanar a ranar Asabar, kamar yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ke sanar da sakamakon da ta tattara zuwa yanzu.

Jami’in da ke tattara sakamakon jihar, wanda kuma shi ne shugaban jami’ar Benin, Farfesa Edogah Omoregie, ya bayyana cewa an dakatar da sanarwar sakamako na ɗan lokaci kafin daga bisani a ci gaba da aikin.

Bayan ci gaban sanarwar, an bayyana sakamakon daga ƙananan hukumomi na Anambra West da Ihiala, inda ɗan takarar jam’iyyar APGA, Soludo, ya ci gaba da jan ragamar nasara a zaɓen.

Ga sakamakon da aka bayyana daga wasu ƙananan hukumomi:

A ƙaramar hukumar Dunukofia, APC ta samu ƙuri’u 3,284, APGA 14,892, LP 71, PDP 16.

A Awka ta Arewa, APC ta samu 3,661, APGA 15,895, LP 299, PDP 203.

A Njikoka, APC ta samu 5,687, APGA 22,213, LP 311, PDP 47.

A Nnewi ta Kudu, APC 9,281, APGA 17,286, LP 73, PDP 12.

A Nnewi ta Arewa APC 5,441, APGA 20,320, LP 1,140, PDP 45.

A Anambra Gabas, APC 3,108, APGA 14,665, LP 304, PDP 207.

A Onitsha Arewa, APC 4,677, APGA 24,225, LP 500, PDP 111.

A Aguata, APC 4,125, APGA 35,559, LP 124, PDP 82.

A Anambra Gabas, APC 16,595, APGA 71,365, YPP 2,871, ADC 152.

 

Sakamakon ya nuna cewa jam’iyyar APGA na kan gaba a yawancin ƙananan hukumomin jihar, inda Soludo ke ci gaba da samun rinjaye mai yawa.

Zaɓen gwamnan Anambra dai ya ja hankalin jama’a saboda yadda yake da muhimmanci ga siyasar yankin kudu maso gabashin Najeriya, kuma hukumar zaɓe ta INEC ta bayyana cewa za ta ci gaba da sanar da cikakken sakamako bayan kammala tattara sakamakon na sauran wurare.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here