Dalibin Jami’ar Bayero dake Kano ya zama gwarzon gasar tarihi ta Afrika.

Screenshot 20231008 125431~2

Dalibin mai suna Abdulmalik Abubakar Isa dan asalin jihar Kano wanda yake karantar ilimin doka da shari’a ya sami nasarar zama gwarzon shekara a gasar tarihi ta Afrika da aka fafata karon karshe a babban birnin tarayya Abuja. Kuma aka nadashi sarautar gwarzon tarihin Africa “Keeper of African History 2023”.

Rahotanni sun nuna cewa dalibin ya fafata a gasar ne cikin adadin kimamin dalibai 2,345 na dukkan Jami’o’in Nigeria inda ya sami nasarar tsallake matakai daban-daban har suka dawo su talatin, wanda kowacce shiyya ta kasar nan ta sami wakilcin mutum biyar-biyar.

Bayan fafata matakin ne suka dawo su biyu a kowace shiyya wanda ya sami nasarar fitowa daga Jami’ar ta Bayero a matakin.

Bayan zazzafar fafatawa ya tsallaka zuwa matakin gwabzawa a tsakanin shiyyoyi inda ya nasarar fitowa a cikin mutane shida kachal. Wanda suka rankaya babbar Jami’ar tarayya ta Calabar dake Birnin Cross River inda ya sami nasarar fitowa a cikin mutane hudu zakarun da zasu tsallaka matakin kusa dana karshe.

Bayan da Jami’ar Bayero ta karbi bakuncin matakin kusa dana karshe inda yayi nasarar tsallakawa matakin karshe tare da abokin karawarsa daya fito daga jami’ar Ilorin dake jihar Kwara.

A fafatawar zagayen karshe da aka gabatar a Jami’ar Nile dake Abjua, ya sami nasarar zama gwarzon gasar inda ya sami nadin sarautar “Gwarzo kuma mairike da kambun tarihin Africa na shekarar 2023”

Ya sami kyaututtuka daya hada da:

1. Tsabar kudi naira Dubu dari biyar
2. Biya masa kudi zuwa kasar Kenya domin yawon shakatawa.
3. Samun kambun zama “Gwarzon Tarihi na Africa” da sauran kyaututtuka.

Dalibin ya bayyana matukar farin cikinsa da godiya ga Allah bisa nasarar daya bashi duk da cewa ba fannin tarihi yake karanta ba, amma tunda gasar ta ƙunshi dukkan dalibai dake karantar kowane fanni, hakan ya bashi damar zama zakara a gasar.

Daga karshe yayi kira ga sauran dalibai da su maida hankali su kara jajircewa domin komai mai iya yiwuwa ne a fannin ilimi domin dalibi baisan wane fanni bane zai zama silar daukaka a gareshiba.

Ya kara da cewa “duk da ina shugaban dalibai masu karantar Shari’a ta Jami’ar Bayero, gashi kuma ina shekarar karshe inda nake kokarin kammala nazarin bincike wato (project), harda ma shugabancin dalibai na mazabata, wato Kaura Goje Students’ Association (KAGSA) dake karamar hukumar Nasarawa, hakan bai hanani jajircewa da maida hankali wajen fadada bincike ba”

“Dole na godewa Allah tare da fatan sauran dalibai zasu dage wajen maida hankali a karatuttukansu baki daya” inji dalibin.

Tun da farko anata bangaren Jami’ar Bayero itama ta Karrama dalibin da lambar yabo, da ta Alumni, da zunzurutun Kudi naira Dubu dari biyu da hamsin wanda shugaban jamiar Vice Chancellor Prof. Sagir Abbas ya gudanar a ofishin sa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here