Wani makaho mai suna Owolabi Adefemi da aka fi sani da Ojunu ya damfari wata mata ‘yar shekara 86 mai suna Madam Alimot tare da yin lalata da ‘yarta da jikanta a jihar Ogun.
An yi zargin cewa mai bada maganin, na sayar da magunguna ganyaye inda ya yaudare ta zunzurutun kudi da nufin samar da waraka ga ‘yar ta da ke fama da rashin lafiya.
Ƙarin cikakkun bayanai masu tayar da hankali sun nuna cewa Adefemi ya yi lalata da ‘yar Alimot, Bose, dakuma jikanta.
Uwargida Alimot, dake Mowe a jihar Ogun, ta gano wanda aka ce mai maganin gargajiya ne bayan ta ji tallan sa a wani gidan rediyon jihar Ogun, inda aka yi masa bushara da basirar sa na sihiri na warkar da cututtuka da kuma hasashen abubuwan da zasu faru a rayuwa, inda matar ta garzaya ga dan-duban a Ogijo domin samun mafita, inda rahotanni suka tabbatar da cewa Alimot ta sayar da gine-ginenta guda biyu don biyan waɗannan buƙatu.
Bose, diyar Alimot, ta amsa laifinta cewa sunyi kwanciyar aure da Adefemi kuma ta yi karin haske game da halin datake fuskanta. “Daga baya Baba Ojunu ya gargade mu da kada mu gaya wa kowa abin da ya faru tsakanin mahaifiyata da shi, inda ya yi barazanar cewa za mu rasa rayukanmu idan ba mu yi biyayya da gargadin nasa ba,” Bose ta bayyana.
Adefemi da ke kokarin rage girman badakalar da ya ke yi, ya ce ya damfari Madam Alimot sama da Naira miliyan 5 ne kawai ba wai Naira miliyan 19 da ake ikirari ba.
“Na kasance ina yaudararsu cewa wani aljani na magana da Mama game da halin da take ciki. Abin da Mama ba ta sani ba, ni ne nake yin karyar muryar wata tsohuwa don in yaudare ta,” inji bokan.
Al’amarin ya bar iyalin cikin dimbin basussuka, da fuskantar bala’in da ya biyo bayan aukuwar lamarin.
Yanzu suna neman adalci, a mayar musu da kudadensu, kuma suna fatan wayar da kan al’umma game da yaudarar mutane irin ta su Adefemi.













































