Majalisar wakilai ta bayyana cewa za ta sake gabatar da kudirin gyaran dokar zabe ranar Laraba.
Shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila ya ce majalisar ta yanke shawarar sake yin aiki da kudirin tare da aikewa da shugaban kasa cikin gaggawa domin ya amince.
Femi Gbajabiamila ya sanar da hakan ne a lokacin da yake jawabi ga mambobin majalisar bayan dawowa daga hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Ya ce an gabatar da zabin fidda gwani na kai tsaye a cikin kudirin domin baiwa gaba daya ‘yan jam’iyyar damar kada kuri’a a yayin zaben fidda ‘yan takara.
Shugaban majalisar ya kuma sanar da fara gyaran kundin tsarin mulki na shekarar 1999 da majalisar ke aiki a kai za a tura zuwa majalisun jihohi domin gudanar da aiki tare kafin karshen watan Fabrairu, 2022.
Shugaban majalisar ya ci gaba da cewa, abin takaici ne yadda ake amfani da gazawar jam’iyyun siyasa wajen samun daidaiton rajistar mambobinsu wajen hana ‘yan Najeriya damar shiga zaben fitar da gwani na ‘yan takara.
Ya kuma ce gazawar jam’iyyun wajen gudanar da sahihin rijistar ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar na 1999 domin ya sa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ke da wahala wajen sa ido kan ayyukan jam’iyyun.
Gbajabiamila ya ce daukar matakin fidda gwani na kai tsaye zai tilastawa jam’iyyun siyasa samun sahihin rijistar mambobin, inda ya kara da cewa kasa da watanni 13 a gudanar da babban zabe, abin da ‘yan Najeriya ke bukata shi ne a samar da sahihin dokar zabe.










































