Shugaba Buhari ya kaddamar da dalar shinkafa a Abuja

WhatsApp Image 2022 01 18 at 1.24.12 PM
WhatsApp Image 2022 01 18 at 1.24.12 PM

Shugaban kasa Muhammadu Buhari kaddamar da dalar shinkafa a wani gagarumin taro da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.

An samar da shinkafar ne ta karkashin shirin Anchor Borrower wanda hadin gwiwa ne tsakanin babban bankin Nigeria CBN da kungiyar manoman shinkafa ta Najeriya RIFAN.

Da yake jawabi a wajen taron Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi farin ciki da nasarar da shirin ya samu, inda ya yabawa masu lura da shirin kan jajircewa da suka yi wajen ganin an samu wannan nasara ta samar da dalar shinkafa  mafi girma a tarihin Najeriya.

Ya kara da cewa gwamnatinsa zata ci gaba da fito da sabbin tsare-tsare domin tallafawa manoma ta yadda zasu iya samar da abincin da zai wadata kasar nan, har akai lokacin da Nigeria za ta yi fice wajen fitar da kayan abinci da ta noma zuwa wasu kasashe.

A nasa jawabin Gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele ya bayyana cewa, duk da kalubalen da aka fuskanta a shekarun baya da suka hada da Tashe-tashen hankula, ‘yan bindiga, da dai sauransu, manoman sun ci gaba da jajircewa, suna yin noma fiye da dogaro da kai kawai, tare da tallafawa gwamnatin shugaban kasa Buhari wajen samar da wadataccen abinci a kasar.

Dalar shinkafar da aka kaddamar a yau tana a matsayin biyan bashin lamuni da manoman RIFAN na shekarar 2020 zuwa 2021.

An kaddamar da shirin Anchor Borrower na CBN a watan Nuwambar 2015, na farko a jihar Kebbi, domin kawo dauki ga manoma da kuma tasiri darajar amfanin gona daban-daban a Najeriya.

Shirin ya kuma kara habaka noman shinkafa mai inganci zuwa tan miliyan 9.5, wanda hakan ya sa Najeriya ta zama kasar da ta fi kowacce kasa samar da abinci a Afirka da kuma ceto Najeriya kudaden waje da kuma adanawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here