Shugaban masu garkuwa da mutane a Zamfara, Bello Turji, ya ajiye makaman sa, inda ya rungumi zaman lafiya a jihar.
Mataimakin gwamnan jihar ta Zamfara , Sanata Hassan Nasiha ne ya bayyana hakan a Gusaun ranar Lahadi.
Ya ce sakamakon tuban da Turji ya yi, an sami zaman lafiya a Birnin Magaji, Shinkafi da kuma karamar hukumar Zurmi.
Mataimakin gwamnan ya bayyana hakan ne a wajin wani taro akan harkokin tsaro da kungiyar daliban jami’ar Medina da ke Saudi Arabia suka shirya.
Ya kuma kara da cewa ya yi taro ma ban ban ta da jagororin yan ta’addan a kanan hukumomi 14 dake jihar, domin wanzar da zaman lafiya mai durewa.
Ya kuma yi addu’ar zaman lafiya mai durewa a jihar da kuma kasa baki daya.













































