JOHESU ta zaɓi sabon shugaba a Kano

IMG 20211201 WA0029
IMG 20211201 WA0029

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ma’aikatan lafiya ta ƙasa JOHESU shiyyar Kano, ta zaɓi sabon shugabanta.

Kwamared Ibrahim Muhammad Maikarfi Shi ne ya lashe zaɓen wanda aka gudanar a sakatariyar ƙungiyar.

Kafin zaɓarsa a matsayin Kwamared Makarfi shi ne shugaban ƙungiyar ma’aikatan jinya da Unguwan zoma na jihar kano Watau Nursing and Midwifery Association Of Nigeria.

Sabon shugaban ya gode wa Allah bisa wannan dama da ƴaƴan ƙungiyar suka ba shi na jagorantarsu, kana ya sha alwashin ci gaba da jajircewa wajen ciyar da kungiyar gaba.

Harka kuma ya buƙaci waɗanda suka nemi matsayin ba su samu ba da su ci gaba da bada gudummuwarsu wajen ciyar da kungiyar gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here