Cibiyar Kula da Cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya NCDC, ta tabbatar da ɓullar cutar Omicron na farko a kasar.
NCDC ta sanar da hakan ne a wata sanarwa da ta fitar da safiyar Larabar nan mai ɗauke da sa hannun daraktan hukumar, Dr Ifedayo Adetifa.
A cewar hukumar, an gano nau’in Omicron a cikin matafiya biyu daga Afirka ta Kudu a makon da ya gabata ta hanyar jerin kwayoyin halitta masu inganci a Cibiyar Kula da Cututtukan.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanya wa sabon nau’in cutar VOC bayan da aka gane yana iya yaduwa tare da ƙarin haɗarin sake kamuwa da cutar.
Darakta Janar na NCDC, Dakta Ifedayo Adetifa, ya buƙaci jihohi da su tabbatar da bin ƙa’idoji matakan rigakafin kamuwa da cutar yayin da ake kara ɗaukar nauyin gwaji da gwaje-gwaje, musamman ta hanyar gwajin gaggawa na Antigen-based Rapid Diagnostic Test RDT.
Ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su yi allurar rigakafi tare da bin ingantattun matakan kariya da suka haɗar da sanya abin rufe fuska wanke hannu akai-akai da tsaftacewa da sauran Matakan kare kai daga kamuwa da cutar.
Ya ce, “A gwajin taa NCDC a ɗakin gwaje-gwajenta na National Reference Laboratory da ke Abuja ta tabbatar da ɓullar cutar ta nau’in Omicron ta farko a Najeriya.
“Binciken kwayoyin cutar da aka yi daga gwaji na kwana biyu na yau da kullun ga duk matafiya zuwa Najeriya sun gano wasu nau’ikan Omicron guda biyu a tsakanin matafiya daga Afirka ta Kudu da suka shigo Najeriya a makon da ya gabata.fiye-tafiye na yau da kullum da ake yi wa matafiya ƙasashen waje ne a cibiyar kula da cututtuka ta Najeriya.













































