Fiye da fasinjoji 20 da suka haɗa da ɗaliban makarantar Madinatu Islamiyya da ke ƙaramar hukumar Bagwai a jihar Kano sun mutu a wani hatsarin kwale-kwale da ya ritsa da su.
Jirgin ruwan ya kife ne a kan hanyarsa daga ƙauyen Badau zuwa garin Bagwai.
Ɗaliban da suka rasu, an ce suna kan hanyar su ne ta halarta bikin Maulidi da ake gudanarwa duk shekara domin tunawa da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad.
A cewar wata majiya a babban asibitin Bagwai, sama da fasinjoji 40 ne da suka haɗa da ɗaliban makarantar Islamiyya.
Majiyar ta ƙara da cewa kawo yanzu an gano gawarwaki kimanin 20 kuma an ajiye su a ɗakin ajiye gawa na asibitin.
Solacebase ta ruwaito cewa a shekarar 2008, fasinjoji 24 ne suka mutu a lokacin da wani kwale-kwale ya kife a kauyen Badau a yayin wani bikin aure.
Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Malam Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ƙara da cewa hukumar kashe gobara na ci gaba da aikin ceto da misalin karfe 9:15 na daren jiya Talata.
A cewarsa ya zuwa yanzu, an gano gawarwakin daliban da abin ya shafa da na sauran fasinjoji 20.
Ya kuma bayyana cewa jirgin na ɗauke da fasinjoji sama da 47 daga cikinsu ama an ceto mutane 7.
“Yayin da muke magana, tawagar masu aikin ceto na can suna aiki kuma ya zuwa yanzu an gano gawarwaki 20 da suka mutu yayin da 7 aka samu da ransu,” in ji shi.













































