Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta rushe zaɓen shugabancin APC da tsagin Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya gudanar.
Dayake zartar da hukuncin, Me sharia Hamza Mu’azu ya tabbatar da zaɓen da tsagin tsohon gwamnan Kano Ibrahim shekarau ya gudanar.
Me Sharia Mu’azu yace zaɓen da tsagin Mallam Shekarau, Kuma Sanatan Kano ta tsakkiya da akaiwa suna G_7, sun gudanar da halastaccen zabuka wanda shugabannin Jam’iya bisa amincewa da sa hannun kwamitin mutane 7 da uwar jam’iyyar ta turo jihar domin gudanar da zaɓen.
Alkalin kotun, Mai shari’a Hamza Muazu yace ya amince da zaben da bangaren Sanata Ibrahim Shekarau suka gudanar da ya samar da Alhaji Ahmad Haruna Zago a matsayin halastaccen shugaban Jam’iyar a jihar.
Jaridar Solacebase ta rawaito cikin waɗanda su ka shigar da ƙarar sun haɗa da Muntaka Bala Sulaiman da mambobin jam’iyyar 17,980, Inda suke ƙarar APC, da shugaban kwamitin rikon Jam’iyar Mai Mala Buni, da sakataren Jam’iyar na riko Sen. John Akpanudoedeha da kuma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC.
Nuraini Jimoh, SAN shi ne lauyan Masu Kara yayin da Sule Usman, SAN, M.N. Duru da Mashood Alabelewe Suka kasance Lauyoyin Waɗanda ake Kara.
Idan za a iya tunawa , Jam’iyar APC karkashin Gwamna Ganduje aranar 31 gawatan yuli ta gudanar da zabukan shugabannin Jam’iyar amatakin kananan hukumomi, Inda ta maido da dukkan shugabannin Jam’iyar 44 tareda bayyana su wadanda suka lashe zabukan ba hamayya.
Sai dai hakan bai yiwa tsagin sanatan ibrahim shekarau dadi ba, lamarin da ya kaiga Dan majalisar tarayya Mai wakiltar birnin Kano Shaaban sharada kê kokawa.













































