
Shugaban kasar Senegal, Diomaye Faye ya zama sabon shugaban taron shugabannin kasashe da na gwamnatocin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS).
Faye ya zama sabon shugaban ne yayin babban taron ECOWAS karo na 69 da aka gudanar a kasar Saliyo.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Kimiebi Imomotimi Ebienfa ne ya tabbatar da hakan a cikin wata takaitacciyar sanarwa da ya fitar.











































