Sama da alhazai miliyan daya sun hau dutsin Arafat don gudanar da aikin hajjin bana.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya rawaitu cewa tsayawa a Arafat na daya daga cikin jiga-jigan aikin Hajji, saboda a gurin Allah baya dawo da duk addu’ar da Alhazai sukayi.
A kuma gurin ne annabi Muhammad SAW, ya gabatar da wa’azin ban kwana ga wa ‘yan da sukai aikin Hajji na shekarar, wanda kuma shine aikin Hajjin sa na karshe a duniya.
Ana sa ran Alhazai zasu yi amfani da wannan rana ta Arfat su yiwa kawunan su addu’a, ‘yan uwan su, muslimai baki daya da kuma kasashen da suka fitu.













































