Majalisar Dattijai ta bada umarnin a samar da Kyamarorin CCTV a duk gidajen Gyaran Halin dake Kasar nan

senate
senate

Majalisar dattawa ta umurci hukumar kula da gyaran hali ta Kasa (NCS) da ta samar da kyamarorin tsaro a dukkanin cibiyoyin ajiya da gyaran hali a cikin kasafin kudinta na 2023 domin magance hare-haren da suke sake afkuwa a kasar.

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis bayan ziyarar tantance ma’aikata da ke Kuje, biyo bayan harin da aka kai a ranar Talata da ya yi sanadin tserewa fursunoni kusan 800.

Lawan ya bayyana kaduwarsa kan yadda ya tarar da gidan babu kyamarorinn tsaro na CCTV inda ya bayyana harin a matsayin abin takaici kuma alama ce ta gazawar tsarin tsaron kasar nan.

“Na yi imanin cewa ya kamata hukumomin tsaron mu su dauki wannan daga tsarin bin diddigin su na Birnin Abuja,” in ji Lawan.

“Mun nemi babban Kwanturola Janar na hukumar da ya tabbatar da cewa bukatar CCTV a manya da matsakaitan cibiyoyin dake kasar na cikin kasafin kudinsu na 2023 saboda wannan yana da muhimmanci kuma babu makawa.

“Yanzu, da yake wannan wurin ba shi da kyamarar tsaro mai aiki, babu wani tarihin abin da ya faru, sai labari. Amma da a ce muna da CCTV, da akalla bayanan zasu kasance a ciki da kuma an yi bincike, kuma za a kama su bisa bayanan da aka samu daga CCTV.”

Lawan ya umarci jami’an tsaro da su tabbatar an dawo da fursunonin da suka tsere daga cibiyar.

Da yake magana tun da farko, kwamandan bataliya ta sojojin Najeriya dake Gwagwalada, Laftanal Kanal Adisa, ya shaidawa majalisar dattawa cewa sama da mutane 300 da ake zargin mahara ne suka kai hari sansanin a ranar Talata.

“Jami’an tsaro 50 ne kawai ke bakin aiki a lokacin da suka zo dauke da bama-bamai da sauran makamai,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here