Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya ce harin da ‘yan ta’adda suka kai gidan ajiya da gyaran hali na Kuje a ranar Talata ya yi nuna matukar gazawa ne ga tsaron kasar nan.
Lawan, ya ce harin da aka kai gidan, zai iya yiwuwa ne kawai tare da hadin gwiwar masu jami’an hukumar ta gidan gyaran hali dake yin liken asiri.
Shugaban Majalisar Dattawa ya kausasa kalamai kan Hukumar Kula bisa rashin samar da na’urorin tsaro daukar hoto na tsaro (wato CCTV) a gidajen gyaran hali dake fadin kasar nan.
Lawan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokacin da ya jagoranci tawagar shugabannin majalisar dattawa domin duba abin da ya faru a gidan gyaran halin.
“Da farko mutum dari uku ba za su zo su yi aiki irin wannan ba ba tare da shiri ba. Dole ne shirin an dauki mako guda, wata daya ko fiye da haka. Na yi imanin cewa ya kamata hukumomin tsaron mu su dauki matakin da ya dace daga tsarin bin diddigin su na birnin tarayya Abuja.
“Na biyu mun ji takaicin cewa wannan wurin ba shi da kyamarorin tsaro (CCTV), wadanda ke daukar cikakken bayani game da abubuwan da ke faruwa tare da nadir abubuwan da suka faru.
“Mun nemi Babban Kwanturola Janar na Cibiyar Gyaran Hali da ya tabbatar da cewa an shigar da bukatar CCTV a cikin kasafin su na 2023 saboda wannan yana da mahimmanci sosai.
“Yanzu, da yake wannan wurin ba shi da CCTV mai aiki, babu wani tarihin abin da ya faru, sai labari. Amma da a ce muna da CCTV, da akalla bayanan sun kasance a can kuma an yi bincike, kuma za a kama su bisa bayanan da aka samu daga CCTV.













































