Daraktan Cibiyar Nazarin Dimokuradiyya ta Aminu Kano da ke Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Habu Mohammed Fagge, ya bayyana damuwarsa kan halin da siyasar Najeriya ke ciki gabanin babban zaben 2027, yana gargadin cewa kasar na iya fuskantar takaici saboda rashin samun wani zabi mai inganci da zai iya fuskantar gwamnatin da ke kan mulki yanzu.
A cikin wata hira da ya yi da SolaceBase, Fagge ya ce yanayin siyasa da kuma tsarin da jam’iyyun siyasa ke bi wajen zabo ‘yan takara baya haifar da ‘yan takara da zasu iya ba ‘yan Najeriya kwarin gwiwa.
A cewarsa, matsain tattalin arziki da ‘yan kasa suke fuskanta tun bayan zaben 2023, tare da hauhawar farashin kayayyaki da talauci da ya shafi kowa, sun haifar da rashin gamsuwa a tsakanin masu kada kuri’a. Duk da haka, ya lura cewa tsarin siyasa a yanzu ba ya nuna zai bai wa ‘yan kasa waninzabi da zai gamsar da su.
“Zaben 2027 zai kasance babban zabe mai cike da matsaloli wanda zai iya kaiwa ga takaici da fushi ga ‘yan Najeriya da yawa,” in ji shi.
Fagge ya yi zargin cewa raunin da ke cikin tsarin zabe da kuma siyasar cikin gida ta jam’iyyu na iya bude kofa ga dawowar masu mulki yanzu duk da karuwar rashin jin dadin jama’a. Ya yi gargadin cewa irin wannan sakamakon na iya kara zurfafa rashin amincewar jama’a da kuma lalata amincewarsu ga tsarin dimokuradiyya.
Masanin siyasar ya ce ‘yan Najeriya da yawa sun rasa amincewa da shugabannin siyasa saboda alkawuran yakin neman zabe da ba a cika ba, yanayin tattalin arzikin da ke ta’azzara da kuma rashin tsaro da ake ci gaba da fuskanta.
Ya kara da cewa sai dai idan jam’iyyun siyasa sun gyara tsarin zabo ‘yan takararsu tare da ba ‘yan kasa zabin da za su iya dogara da shi, kasar na cikin hadarin shiga wani zagaye na sabon yanayin siyasa da raguwar amincewar jama’a ga gwamnati.
Fagge ya bukaci masu ruwa da tsaki da su karfafa tsarin dimokuradiyya tare da tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin zabe domin dawo da amincewar jama’a kafin zaben 2027.













































