Sarkin Musulmi ya umarci Musulmai su fara neman watan Jumada Ula

Sultan of Sokoto

Majalisar sarkin Musulmi a Sakkwato ta umarci dukkan Musulmai a faɗin ƙasar nan da su fara neman sabon watan Jumada Ula na shekarar Hijira ta 1447AH daga yammacin Talata, 21 ga Oktoba, 2025, wanda ke daidaita da ranar 29 ga watan Rabi’ul Thani 1447AH.

Wannan umarni yana cikin wata sanarwa da Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na majalisar, ya sanyawa hannu a ranar Litinin.

Sanarwar ta bayyana cewa Musulmi su fara kallon sararin samaniya daga yammacin Talata domin neman sabon watan, sannan duk wanda ya gani ya sanar ga hakimin gunduma ko na gari mafi kusa da shi.

A cewar sanarwar, rahotannin da aka tattara za a mika su zuwa ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, wanda shi ne shugaban majalisar koli ta ƙasa ta harkokin Musulunci (NSCIA).

Farfesa Junaidu ya yi addu’ar neman taimako da jagorancin Allah wajen gudanar da wannan muhimmiyar ibada, yana mai fatan Allah Ya karɓi kokarin Musulmi.

Neman sabon watan Jumada Ula yana nuni da farkon sabon watan Musulunci wanda ake amfani da shi wajen tsara lokutan ibada da sauran ayyukan addini na Musulmi a kalandar Hijira.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here