Kungiyar Fridabs Solacebase Communications, karkashin jaridar Solacebase ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki game harkar lafiya a jihar Jigawa.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa ta shirya taron ne da nufin inganta ayyukan kiwon lafiya tun daga tushe.
Da yake jawabi tun da farko a wajen taron mai taken,” Ci gaban Kiwon Lafiyar Jama’a ta hanyar hada hannu” mawallafin jaridar Solacebase, Abdullateef Abubakar Jos, ya ce taron an shirya shi ne domin magance kalubalen da ke tattare da samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya a yankunan karkara da kuma shirin ko ta kwana game da barkewar annoba a jihar.
“Tare da ziyarar da muka kai wa wasu kananan asibititoci a wasu yankunan jihar Jigawa, mun yi imanin cewa jama’a da gwamnati za su iya tattaunawa kan abubuwan da ya kamata a yi don inganta harkar kiwon lafiya tun daga tushe.”
A nasa bangaren, wani kwararre a fannin kiwon lafiya, Dakta Muhammad Namadina dake aiki a asibitin koyarwa na Aminu Kano, ya yi kira da a hada kai tsakanin gwamnati da al’umma a matsayin wani mataki na inganta harkokin kiwon lafiya a yankunan karkara.
Ya bukaci gwamnati da ta ba da fifiko kan shirye-shiryen annoba tare da wayar da kan jama’a kan matakan da za su dauka idan an samu barkewar annobar da kuma tura kayan aiki cikin hadin gwiwa domin cimma nasara.
Wasu daga cikin mahalarta taron wadanda ma’aikatan kiwon lafiya ne sun koka bisa rashin karfafa gwiwa daga gwamnatin jihar ga ma’aikatan lafiya.
“Daya daga cikin babbar matsalarmu ita ce rashin samun ci gaba da kuma karfafa gwiwa da za su iya sanya mutum yin aiki tukuru,” in ji kwararrun ma’aikatan lafiya.
Har ila yau, wasu daga cikin mahalarta taron sun nuna damuwa kan rashin isassun ma’aikatan lafiya a cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko da ke jihar.
Shi ma a nasa jawabin, bulaliyar majalisar dokokin jihar Jigawa, Alhaji Lawan Garba Muhammad ya ce majalisar a ko da yaushe tana goyon bayan gwamnatin jihar a ayyukan da za su inganta harkokin kiwon lafiya a jihar.
“Tallafin da majalisar ta baiwa bangaren zartarwa a matsayin matakin magance karancin ma’aikata sun hada da dokar kafa karin kwalejojin aikin jinya guda biyu a Hadejia da Babura tare da inganta na Birnin-Kudu,” inji Muhammad.
Muhammad ya kuma yaba da shirin da masu ruwa da tsaki suka yi na samar da hanyoyin inganta harkokin kiwon lafiya a Jigawa.
Mahalarta taron sun hada da shugabannin al’umma da kungiyoyin fararen hula da ma’aikatan lafiya da ‘yan majalisa, da kuma jami’an tsaro.
Kazalika, Fridabs Solacebase Communications ta kuma gudanar da wani taron wayar da kan jama’a da bayar da shawarwari tare da karfafa gwiwa, ga daliban makarantar koyon aikin jinya da ungozoma ta Birnin Kudu dajke Jihar Jigawa, a ranar Larabar da ta gabata.














































