Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 11 da kuma Talata 12 ga watan July na shekarar 2022 a matsayin ranar hutun Babbar Sallah.
Ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, shine ya sanar da hutun, ya kuma taya Musliman Najeriya murnar Babbar Sallah.
Ya kuma yi kira ga musilmai dasu cigaba da koye da shugaba annabi Muhammad (SAW), tare da nuna kauna, zaman lafiya da juna, da kuma yiwa kasa addu’a don samun zaman lafiya mai durewa a kasa baki daya.













































