‘yan bautar kasa 13 aka karawa shekara daya na bautar kasar su a jihar Nasarawa, saboda wasa da aikin da aka tura su.
Jami’in hukumar ta NYSC a jihar Nasarawa, Abdullahi Jikamshi ne ya sanar da hakan yayin yaye ‘yan bautar kasa na rukunin (B), daga sansanin bautar kasar.
Ya kuma yi addu’a ga ‘yan bautar kasar da suka rasa rayukansu yayin gudanar da aikin su, sanan yayiwa wa ‘yan da aka yaye murna, tare da yi musu fatan Alkairi.
A nasa bangaren, gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya yabawa hukumar ta NYSC bisa gudunmawar da suke bawa jihar sa.













































