Mashawarci na Musamman ga Gwamnan Jihar Kano kan Ilimin Tsangaya, Sheikh Musa Falaki, ya zargi tsohon Mataimakin Gwamna, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, da karkatar da Naira miliyan 308 da kananan hukumomin Kano 44 suka bayar domin gudanar da addu’o’i na musamman.
Falaki ya yi wannan zargin ne a wata hira da aka watsa a gidan rediyo, inda ya ce an tattara kudaden da aka ware don ayyukan addini a fadin jihar da sunan malamai wadanda ba su karbi kudin ba kuma ba su gudanar da addu’o’in ba.
A cewarsa, tsohon shugabancin Kungiyar Kanana Hukumomin Najeriya (ALGON) reshen jihar Kano ya sanar da su cewa kananan hukumomi 44 na ba da gudummawar Naira miliyan 44 a kowane wata domin daukar nauyin addu’o’i na musamman.
Ya ce an tsara cewa shi da Sheikh Ibrahim Sheshi Maihula ne za su jagoranci shirin.
“An ce kananan hukumomi suna ba da gudummawar Naira miliyan 44 a kowane wata domin addu’o’i na musamman a fadin jihar, kuma an sanar da mu cewa Sheikh Ibrahim Sheshi Maihula da ni ne za mu jagoranci shirin,” in ji Falaki.
Sai dai ya yi zargin cewa babu malami daya da ya karbi sisi daga kudaden da suka shafi shirin.
Falaki ya ce ba su da labarin an fitar da kudi da sunansu sai bayan da Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta gayyace su a matsayin wani bangare na binciken da ke gudana.
“Mun yi mamaki lokacin da hukumar ta gayyace mu, a can ne muka gano cewa an fitar da kudi da sunan mu domin addu’o’in,” in ji shi.
A cewar sa, masu bincike sun sanar da su cewa an fitar da Naira miliyan 44 a kowane wata tsawon watanni bakwai, wanda hakan ya kai jimillar Naira miliyan 308.
Ya jaddada cewa tun da malamai ba su karbi kudin ba kuma ba su shirya addu’o’in ba, ba zai yiwu a yi amfani da kudin don abin da aka shirya ba.
Falaki ya kara da cewa lamarin na daga cikin manyan binciken da hukumar yaki da cin hanci ke yi kan yadda ake gudanar da kudaden kananan hukumomi.
Ya zargi cewa masu bincike sun bukaci Gwarzo da ya mayar da fiye da Naira miliyan 700 da ake zargin an karkatar daga asusun kananan hukumomi 44.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, tsohon mataimakin gwamnan bai yi wani martani a bainar jama’a kan zargin ba.












































