Ofishin jakadancin Amurka da ke Legas ya bayyana cewa, ba haƙƙi ba ne samun takardar shigar ƙasar Amurka ga baƙin ƙasa, sai dai gata ne da gwamnati ke bayarwa bisa ikon ta.
Ofishin jakadancin ya yi wannan bayani ne ranar Alhamis a cikin amsar da ya bai wa jaridar The Punch game da soke takardar shigar ƙasar da aka bai wa fitaccen marubuci kuma mai lambar yabo ta Nobel, Farfesa Wole Soyinka.
A cikin sakon imel ɗin da ma’aikaciyar hulɗa da jama’a ta ma’aikatar harkokin waje ta Amurka, Julia McKay, ta aikawa jaridar, ta bayyana cewa doka ta hana su bayyana cikakkun bayanai kan batun takardar shigar da aka soke saboda sirri.
Ta kuma ce gwamnati na da ikon soke takardar Bisa kowanne lokaci idan ta ga dama, domin takardar shigar ƙasar gata ce, ba haƙƙi ba, kamar yadda kowace ƙasa ke da ikon tantance wanda zai shiga cikin ƙasarta.
Labari mai alaƙa: Dalilin da yasa Amurka ta soke Bisa ta dindindin – Soyinka
A ranar Talata a Legas, Soyinka ya bayyana wa manema labarai cewa ofishin jakadancin Amurka ya sanar da shi soke takardar Bidar sa ta nau’in B1/B2, inda ya ce daga yanzu bai da damar shiga ƙasar.
Ya nuna mamaki kan matakin, yana mai cewa bai taɓa aikata wani laifi da zai sa a soke masa izinin shiga Amurka ba.
Farfesan ya tuna wasu tsoffin abubuwa guda biyu da suka faru shekaru da dama da suka wuce, inda ɗaya ya shafi rashin bayyana kayan miya a filin jirgin sama a Chicago, yayin da ɗaya kuma ya kasance muhawara da jami’an tsaro a wani otal a Atlanta shekaru da dama da suka gabata.
Sai dai ya ce bai yi imani cewa waɗannan abubuwan ne suka jawo soke takardar shigar ba.
A wasikar da ofishin jakadancin Amurka ya aika masa, an bayyana cewa an soke takardar shigar sa bisa tanadin doka ta sashen 22 CFR 41.122, saboda sabbin bayanai da suka fito bayan an bashi takardar.
An kuma bukace shi da ya mayar da ita domin a soke ta a zahiri.
Farfesa Soyinka, wanda ya lashe lambar yabo ta Nobel a fannin adabi a shekara ta 1986, ya shafe dogon lokaci yana rayuwa a ƙasashen waje, musamman Amurka, inda ya koyar a jami’o’i daban-daban.
Soke takardar shigar tasa ya janyo sabbin tattaunawa game da matakan da Amurka ke ɗauka kan ƙuntata shigowar baki daga Afirka.













































