Gwamnatin tarayya ta fara rabon tallafin ma’aikatan manyan makarantu

Alausa education minister

Gwamnatin tarayya ta fara rabon kuɗaɗe a ƙarƙashin shirin tallafin ma’aikatan manyan makarantu (TISSF), wanda aka ƙirƙira domin ƙarfafa walwalar ma’aikata, haɓaka aiki da ƙirƙira a fannin ilimi a ƙasar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktar yaɗa labarai da hulɗa da jama’a ta ma’aikatar ilimi ta tarayya, Folasade Boriowo, ta fitar a Abuja ranar Juma’a, inda ta ambato ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa, yana cewa wannan shiri na cikin manufofin Sabunta Fata na shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Karin labari: Darasin Lissafi ba zai zama dole ba ga ɗaliban ilimin fasaha masu neman shiga jami’a – gwamnatin tarayya

Dakta Alausa ya bayyana cewa shirin ya fita daga matakin tsari zuwa aiwatarwa gaba ɗaya, inda sama da ma’aikata 9,000 na manyan makarantu suka amfana a shekarar farko, wanda ke wakiltar kashi 28 cikin 100 na mutane 33,000 da aka tantance daga jami’o’i, kwalejoji da sauran cibiyoyi 219 na tarayya da jihohi.

Ya ce rabon farko ya haɗa da ma’aikatan koyarwa da marasa koyarwa a tsarin rabo na 30 da 70, wanda ke nuna adalcin gwamnati wajen tallafa wa dukkan nau’o’in ma’aikata a fannin ilimi.

Dakta Alausa ya bayyana cewa wannan shiri ba wai bayar da kuɗi kaɗai ba ne, amma wani jari ne na haɓaka tattalin arzikin ilimi, domin dawo da mutuncin ma’aikata, girmama sadaukarwa, da gina sabon tushe ga ilimin ƙasa.

Ya ƙara da cewa ma’aikatar ta kuduri aniyar gudanar da shirin cikin gaskiya da bayyana bayani a kai, tare da buga rahotanni a kowane kwata na shekara, da tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗin yadda ya dace domin faɗaɗa damar amfana da shirin a gaba.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa an ƙaddamar da shirin ne a watan Agusta 2025, bayan taron manyan masu ruwa da tsaki a watan Yuli, kuma yana daga cikin muhimman sassa na shirin sabunta fannin ilimi na gwamnatin tarayya (NESRI).

Shirin zai bai wa ma’aikata damar samun rancen har zuwa naira miliyan goma ba tare da ruwa ba, domin biyan buƙatu kamar gida, lafiya, ilimi, sufuri da kuma ƙananan kasuwanci.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here