Filin jirgin sama na Malam Aminu Kano ya gudanar da taron tunawa da cika shekaru ɗari da saukar jirgi na farko a Najeriya, wanda ya nuna muhimmancin Kano wajen kafa tarihin sufurin jiragen sama a ƙasar.
Bikin wanda cibiyar horar da matukan jirgi ta Caliphate Aviation Training Centre ta shirya, ya fara ne a ranar Alhamis tare da nune-nunen tarihi, tattaunawa, da gasar tashi da saukar jirage domin ƙarfafa matasa su shiga sha’anin harkar jirgin sama.
A yayin taron, mai kula da filin jirgin sama na yankin, Okikiri Musa, ya bayyana cewa wannan rana ce ta alfahari ga Kano da kuma Najeriya baki ɗaya, inda ya ce samun damar saukar jirgi na farko a Kano wani abin tarihi ne da ya cancanci murna.
Haka kuma, daraktan gudanarwa na Caliphate Air Services, Hassan Abdulhamid, ya ce bikin bai tsaya ne kawai don tunawa da tarihi ba, har ila yau yana nufin karfafa matasa su shiga aikin sufurin jirgin sama ta hanyar koyon dabaru da mu’amala da masana’antar kai tsaye.
Ya bayyana cewa kwanaki biyu na farko na taron an ware su ne domin ɗaliban sakandare, yayin da ɗaliban jami’a da malamai za su gabatar da nazarce-nazarcen da za su taimaka wajen cike gibin bayanai a fannin sufurin jiragen sama a Arewa.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa masanin tarihin sufuri daga jami’ar Bayero da ke Kano, Dakta Yusuf Madugu, ya bayyana cewa jirgi na farko da ya sauka a Najeriya ya iso Kano ne a ranar ɗaya ga watan Nuwamba, shekara ta 1925, daga ƙasar Masar ta hanyar Khartoum da N’Djamena, inda ya sauka a filin wasan doki na Kano (Polo Club) saboda babu filin jirgi a wancan lokaci.
Bikin ya kuma ƙunshi nune-nunen tarihi kan ci gaban harkar jirgin sama a Najeriya, tattaunawa kan rawar da fannin ke takawa wajen bunƙasa tattalin arziki, da kuma tunawa da wadanda suka kafa tarihi a wannan bangare, tare da nune-nunen jirage kai tsaye da wasanni domin nishaɗantar da jama’a.
A gefe guda kuma, an gudanar da gasar tashi da saukar jirgi, gasa ta yara ta kite, da kuma nune-nunen jirage kai tsaye













































