Wutar Lantarki Ta Kara Daukewa A Najeriy, 0 Megawatt 

Blackout
Blackout

Injinan Wutan lantarkin Najeriya sun durkushe zuwa 0Megawatt kaf misalin karfe 10:51 na safiyar Litnin, 26 ga watan Satumba, 2022.

Hakan ya sabbaba rashin lantarkin da ake fama da shi a fadin Najeriya. A bisa bayanan da aka samu, tashar raba wutan lantarkin TCN Afam IV kadai ke aiki amma babu wuta ko daya.

Kamfanonin raba lantarki (DisCos) sun sanar da kwastamominsu bisa aukuwar wannan lamari.

Misalin jami’in yada labaran kamfanin lantarkin Enugu EEDC yace a fadin tarayya ake fama da matsalar rashin wutan.

A cewarsa “Kamfanin raba wutar lantarkin Enugu (EEDC) na sanar da kwastamominta cewa lalacewar wutan da ya auku misalin karfe 10:51 na safiyar yau, 26 ga Satumba, 2022, ya yi sanadiyar dauke wutan da ake fama da shi a fadin tarayya.”

Hakazalika kamfanin wutan Benin BEDC ya sanar da mazauna yankin Edo, Delta, Ekiti, Ondo da kewaye.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here