Jam’iyar APC ta dage lokacin kaddamar da Kwamitin yakin neman zaben ta

APC Convention
APC Convention

Jam’iyyar APC ta sauya lokacin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa mai mambobi 422 da aka shirya fara aiwatarwa a ranar Litinin 26 ga watan Satumba zuwa Laraba 28 ga watan Satumba.

Kakakin Kwamitin yakin neman zaben Mista Onanuga ne ayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a karshen mako a Abuja.

“Kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC na sanar da duk mambobin da aka zaba domin yin aiki a Kwamitin daraktoci daban-daban da su kai rahoto a hedikwatar yakin neman zaben ranar Laraba 28 ga Satumba, 2022 da karfe 8 na safe.

Ya ce za a gudanar da tattakin zaman lafiya bayan an kammala adduoi, yana mai cewa duk wadanda aka zaba za a ba su takardar nadin na su a rana guda.

Onanuga daganan ya taya mambobin kwamitin yakin neman zaben murna, inda ya kira agaresu da su yi wa jam’iyyar hidima tareda sadaukarwa.

“Muna kuma son yin amfani da wannan dama don nuna godiyarmu ga duk kungiyoyin tallafi da suka yi rajista da hukumar yakin neman zaben.

Onanuga ya bukaci kungiyoyin da su ci gaba da gudanar da ayyukansu, inda ya kara da cewa Kwamitin zai yi aiki tare da kungiyoyin yayin da ta shiga kakar yakin neman zabe.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya rawaito cewa, bisa jerin sunayen mambobin majalisar da jam’iyyar ta fitar tun farko, shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai jagoranci babban Kwamitin.

Sanata Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023 da Sanata Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar na kasa za su kasance mataimakan shugabanni.

Gwamna Simon Lalong na Filato kuma shi ne Darakta Janar tare da James Faleke a matsayin Sakataren Majalisar.

Ayayin da Sen. Kashim Shettima dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar shine mataimakin shugaban karamin Kwamitin, inda Adams Oshiomhole tsohon shugaban jam’iyyar APC ke a matsayin mataimakin darakta Janar bangaren Ayyuka yayin da Hadiza Usman ta zamo mataimakiyar darakta-Janar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here