Tawagar daliban jihar Katsina dasuka wakilci Najeriya a gasar cin kofin muhawara ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia sun samu nasarar lashe gasar bayan da ta doke takwararta ta Malaysia mai masaukin baki.
Tawagar Daliban Katsinan ta samu tikitin wakilcin Najeriya ne bayan da ta zama ta biyu a gasar muhawara ta shugaban kasa tsakanin Makarantu da aka yi a Legas a shekarar 2021.
Kakakakin hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Katsina Malam Aminu Badaru ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a karshen mako.
Ya ce an gudanar da muhawarar ne kan al’amuran yau da kullum musamman rikicin abubawan dake faruwa a Rasha da Ukraine, Makarantun Gwamnati da masu zaman kansu da kuma kan tsarin gwamnati.
A cewarsa, gasar da aka gudanar tsakanin 14 zuwa 22 ga watan Satumba, an gudanar da ita cikin nasara ba tare da samun wata tangarda ba.
Badaru ya kara da cewa, “dalibai shida daga kananan makarantun sakandire da ke jihar ne suka wakilci Najeriya a gasar inda hudu daga cikinsu su ka kasance mata.
Ya ce Shugaban Hukumr ilimin bai daya, Alhaji Lawal Buhari-Daura wanda ya jagoranci tawagar, ya bayyana kwazon ‘yan Najeriya a matsayin abin al’ajabi kuma sun dace a yaba musu.
Shugaban Hukumar daganan ya kuma yabawa gwamnatin jihar bisa daukar nauyin tafiyar da ya baiwa jihar damar wakiltar Najeriya yayin muhawarar.
Sanarwar ta ce tuni tawagar daliban ta koma gida.













































