ASUU ta yi barazanar tafiya yajin aiki sakamakon rashin gudanar da mulki a wata jami’a ta Kano 

KUST NEW 3

Kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) reshen jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, Kano, ta bayyana shirinta na shiga yajin aiki idan gwamnati ba ta biya bukatunta ba.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa kungiyar ta nuna rashin jin daɗi kan yadda shugabancin jami’ar ke tafiyar da al’amura, tana zargin akwai rashin gaskiya, rashin bin doka da kuma rashin bayyana ainihin yadda ake kashe kuɗaɗe.

Kungiyar ta bayyana haka ne bayan wani taron da ta gudanar a ranar Alhamis, inda ta nuna damuwa da yadda jami’ar ta kasa inganta yanayin aiki da karatu ga malamai da ɗalibai.

A cikin wata sanarwa da shugaban ASUU na jami’ar, Dakta Aliyu Yusuf Ahmad, tare da sakataren ta, Dakta Abubakar Ibrahim Tukur, suka sa hannu, kungiyar ta zargi mahukuntan jami’ar da kin fitar da asusun da aka duba na shekarun 2023 da 2024, da kuma rahotannin kasafin kudi daga Janairu 2020 zuwa Disamba 2024, wanda hakan ya saba da dokar kafa jami’ar ta 2017.

Kungiyar ta kuma zargi shugabancin jami’ar da kasa fitar da bayani kan wasu kuɗaɗen da aka kashe a kasafin kudi na kwata na farko da na biyu na shekarar 2025, tare da kin ɗaukar sabbin malamai musamman a sabbin sassa da aka buɗe.

ASUU ta ƙara bayyana cewa jami’ar ta kasa dawo da wutar lantarki a dukkan sassan ta, da kuma biyan hakkokin da wasu malamai ke bi tun tuni.

Kungiyar ta roƙi shugabannin jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki su matsa wa shugaban jami’ar lamba don a magance matsalolin cikin gaggawa domin gujewa rikicewar aiki a jami’ar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here