Alamu sun nuna cewa rikicin da ya shiga tsakanin sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ƙare bayan ta aikewa Akpabio da sauran sanatoci gayyata zuwa bikin kaddamar da ayyuka a jihar Kogi mako mai zuwa.
Gayyatar, wadda Natasha da kanta ta sanya hannu a kai, an karanta ta a zaman majalisar ranar Alhamis ta hannun shugaban majalisar dattawa.
A cikin wasikar, Natasha ta gayyaci abokan aikinta sanatoci zuwa garin Ihima a jihar Kogi ranar Lahadi domin kaddamar da ayyukan mazabar da suka zo daidai da cika shekara biyu tana wakilci a majalisar dattawa.
Wasikar ta bayyana cewa wurin taron zai kasance a gidanta da ke Plot 101, Jimoh Akpoti Street, Ihima, Okene, jihar Kogi.
Haka kuma sanatocin da za su tashi ta jirgin sama za su iya sauka a filin tashin jirgin sama na Obajana kafin su ci gaba da tafiya zuwa Ihima ta mota.
Bayan karanta wasikar, Akpabio ya nuna farin ciki inda ya taya Natasha murna, abin da ake kallon sa a matsayin matakin da ya tabbatar da cewa an warware sabanin da ya shiga tsakaninsu tun farkon shekarar nan.
Idan za a iya tunawa, rikicin ya samo asali ne daga batun sauya kujeru a cikin zauren majalisar, wanda ya kai ga dakatar da Natasha na tsawon watanni shida a ranar 6 ga Maris, 2025.
Amma tun bayan dawowarta a watan Satumba, ta ci gaba da halartar zaman majalisa tare da yin mu’amala cikin natsuwa da shugaban majalisar.
Matakin nata na gayyatar Akpabio da sauran sanatoci zuwa bikin kaddamar da ayyuka ya nuna cewa dangantakar da ta taɓa yin tsamari tsakaninsu ta dawo yadda take.













































