Gwamnan jihar Plateau State, Caleb Mutfwang, ya tabbatar da cewa mutane 28 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a yankin Angwan Rukuba da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.
A cikin jawabin da ya gabatar ga al’ummar jihar, gwamnan ya bayyana harin a matsayin abin takaici kuma marar ma’ana, yana mai jaddada cewa waɗanda suka aikata laifin ba za su tsira daga hukunci ba.
Harin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi inda aka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu. Gwamnatin jihar ta nuna alhini tare da jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu, tare da addu’ar samun juriyar jure wannan babban rashi.
Ya bayyana cewa duk da wannan matsalar tsaro, jihar ba za ta yarda ta shiga tsoro ko razana ba, yana mai cewa za su ci gaba da ƙarfafa matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi tare da tabbatar da zaman lafiya.
Bayan faruwar lamarin, gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa ciki har da sanya dokar hana fita ta sa’o’i 48 a ƙaramar hukumar domin bai wa jami’an tsaro damar gudanar da bincike da dawo da doka da oda.
Gwamnan ya kuma ziyarci wurin da harin ya faru da kuma waɗanda suka jikkata a asibitin koyarwa na jami’ar Jos, yana mai cewa gwamnati za ta ɗauki nauyin kula da lafiyarsu tare da tallafa wa iyalan waɗanda suka rasu.
Ya umarci jami’an tsaro su tsaurara aiwatar da dokar hana zirga-zirgar babura a cikin shirin babban birnin Jos, tare da kira ga jama’a su kasance masu lura da kai rahoton duk wani abu da ke da alamar barazana ga tsaro.













































