Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya koma babbar kotun jihar domin ci gaba da shari’ar da ake yi masa kan zargin almundahana da kuɗi.
An ga El-Rufai yana shiga harabar kotun ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro, inda jami’an tsaro suka mamaye wurin yayin da aka fara zaman shari’ar.
Rahotanni sun nuna cewa bayan wannan zaman, ana sa ran zai wuce zuwa babbar kotun tarayya da ke Kaduna domin sauraron bukatar belinsa.
Komawar tasa kotu ta biyo bayan sakin sa na wucin gadi da hukumar ICPC ta yi masa.
An ba shi wannan damar ne domin halartar jana’izar mahaifiyarsa, Hajiya Umma El-Rufai, wadda ta rasu a birnin Alkahira na ƙasar Masar.
Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken sharuddan da aka ɗaura masa ba yayin sakin na wucin gadi, kuma ba a sani ba ko zai ci gaba da zama a waje ko kuma za a mayar da shi hannun hukumar yayin da shari’ar ke ci gaba.











































