Muhammadu Sanusi II Ya Fayyace Dalilan Zuwan Sa Aso Rock da Abin da Ya Fadawa Tinubu 

89008170 2915191471871214 4684438027072700416 n
89008170 2915191471871214 4684438027072700416 n

Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II ya yabi Bola Ahmed Tinubu a dalilin karfin halin da ya yi wajen janye tsarin tallafin man fetur. Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya kuma jinjinawa Shugaban kasa bayan da ya yi fatali da bambanci wajen farashin kudin ketare.

Sanusi II ya bayyana matsayarsa ne a yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya hadu da Mai girma shugaban kasa a ranar Alhamis.

Tsohon Sarkin ya bayyana Bola Tinubu a matsayin abokinsa wanda ya ce ya kama hanyar gyara kasa, ya ce a dalilin hakan ne ya kawo masa ziyara.

“Dalilin farko shi ne in zo in taya shi murna a hukumance. Sannan kuma da yake ina dauke da huluna da-dama, ina sanye da hular masanin tattali saboda haka na zo in gode masa a kan matakan da ya dauka domin farfado da tattalin arzikin nan. Kuma kamar yadda aka san abubuwan da mu ke magana a kai: tallafin man fetur ya zama ala-ka-kai, bambancin farashin kudin kasar waje da sauransu.

Wadannan su ne abubuwan da ni na ke magana a kai na tsawon lokaci, kuma na yi farin ciki da a ranar farkonsa ya tabo su, ‘yan kasuwa su na murna.”

“Saboda haka ya fara da kyau, idan ana maganar tattalin arziki ne, an fara da kafar dama. Mun zo ne domin mu mara masa baya, kuma mu karfefe shi.

Bola Tinubu ya cigaba a wannan hanya, kuma ya tsaya a kan manufofin da yake kai.

Muhammadu Sanusi II Khalifan Tijjaniyan ya ce ya kawo maganar kashe makiyaya 37 da sojojin sama su ka yi a jihar Nasarawa, ya bukaci gwamnatin tarayya tayi bincike. Sanusi II ya ce ya na so gwamnati ta magance sabanin da ke tsakanin makiyaya da manoma.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here