Ranar Ma’aikata: Gwamna Yusuf ya ba da tabbacin sake fasalin aikin gwamnati a Kano

IMG 20250501 WA0145 720x430 (1)

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa ta fara yin garambawul da nufin farfado da harkokin ma’aikatan gwamnati, da kula da fansho, da kuma samar da horo ga ma’aikata a kullum.

Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a jawabinsa a wajen bikin ranar ma’aikata da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha, Kano.

Ya bayyana bikin a matsayin girmamawa ga tarihin gwagwarmayar neman hakkin ma’aikata, mutunci, da adalci, yana mai cewa ranar ta wuce ranar hutu.

“Yau ba ranar hutu ba ce kawai, rana ce da ta samo asali daga sadaukarwa da kuma neman adalci, daidaito, da mutuncin aiki,” in ji shi.

Gwamnan ya kara da cewa jihar Kano ce jiha ta farko da ta fara gudanar da bikin ranar Mayu a shekarar 1980 a karkashin marigayi Gwamna Abubakar Rimi, kuma ya yi alkawarin dorewar wannan abin da aka bari ta hanyar manufofin da suka mayar da hankali kan jin dadin ma’aikata.

Yusuf ya sanar da cewa gwamnatin jihar ta amince da sabon mafi karancin albashi na ₦71,000 ga ma’aikatan gwamnati, wanda hakan ya sanya jihar Kano a cikin jihohin da suka fara aiwatar da karin albashin.

Karin karatu: Ranar Ma’aikata: Tinubu ya sha alwashin ba da fifiko ga jin dadin ma’aikata

Gwamnan ya bayyana wasu muhimman tsare-tsare da suka shafi farfado da ma’aikatan gwamnati da suka hada da samar da horo na yau da kullun da kuma kara kuzari ta hanyar bita da hadin gwiwa da cibiyoyi irin su Kwalejin Ma’aikata ta Najeriya (ASCON).

Ya bayyana cewa gwamnatin sa tana kuma duba muhimman takardu na aiki kamar su Dokokin Ma’aikata, Ka’idojin Kudi, da Tsarin Ma’aikata don ganin sun dace da ingantattun ayyuka.

A cewarsa, ana sa ran sauye-sauyen za su inganta ayyukansu, da inganta da’a, da kuma daidaita ayyukan hidima a ma’aikatu, da hukumomi.

Gwamnan ya ce ana yin irin wannan garambawul a tsarin fansho domin tabbatar da biyan ma’aikatan da suka yi ritaya cikin lokaci kuma cikin adalci.

Yusuf ya jaddada kudirinsa na tabbatar da gaskiya, sanin ya kamata, da kuma jin dadin ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho, yana mai bayyana su a matsayin jigon samun nasarar ayyukan gwamnati.

Ya bukaci hadin kan masu ruwa da tsaki a ma’aikatun gwamnati domin samun nasarar aiwatar da sauye-sauyen. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here