Ranar Ma’aikata: Tinubu ya sha alwashin ba da fifiko ga jin dadin ma’aikata

Bola Tinubu budget

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatin sa ta jajirce wajen ba da fifiko ga jin dadin ma’aikatan Najeriya.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wani sako da ya fitar a shafinsa na X don bikin ranar ma’aikata ta 2025, inda ya amince da muhimmiyar rawar da ma’aikata ke takawa wajen ci gaban kasa.

“Ga kowane ma’aikacin Najeriya, ranar ma’aikata ranar arin ciki ce, domin su ne injin tattalin arzikinmu kuma sirrin ci gaban al’ummarmu, gwamnatinmu za ta ci gaba da ba da fifiko ga jin dadin ma’aikata, kuma tare za mu sake mayar da Najeriya mai girma. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here