FIFA ta amince da kasashe 48 su halarci gasar cin kofin Duniya ta Mata a shekarar 2031

FIFA FIFA

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta ce za ta kara yawan kasashen da zasu halarci gasar cin kofin Duniya ta Mata da za a gudanar a shekarar 2031.

Hakan na cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na Intenet a ranar juma’a 09/05/2025 bayan wani taron tattaunawa da mahukuntan ta suka gabatar.

A cewar FIFA za ta kara kasashen ne daga 32 zuwa 48, inda za a raba rukunin kasashen zuwa 12.

Hakan zalika hukumar ta ce za a kara yawan wasannin da ake daga 64 zuwa 104, kamar yadda za a kara a gasar kofin Duniyar ta Maza a shekara mai kamawa ta 2026.

Za dai a gudanar da gasar cin kofin Duniyar ta Mata a shekarar 2027 a kasar Brazil inda kasashen 32 za su halarta.

A gasar cin kofin Duniyar da aka gudanar a kasashen Australia da New Zealand a shekarar 2023 ne dai aka kara yawan kasashen dake halartar ta daga 24 zuwa 34.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here