Hukumar gudanarwa ta ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sanar da dakatar da mai ba da shawara na fasaha na ƙungiyar, Ogenyi Evans, da babban koci, Ahmed Garba, saboda rashin gamsasshen sakamakon da ƙungiyar ke samu a kakar Gasar Kwallon Ƙafa ta Firimiya ta Najeriya (NPFL) ta shekarar 2025/2026.
A cikin sanarwar da sashen yada labarai na ƙungiyar ya fitar a Kano, ya ce dakatarwar ta fara aiki nan take, kuma manufarta ita ce sake tsara tawagar domin samun sakamako mafi kyau a wasannin gaba.
Hukumar ta bayyana cewa ƙungiyar ta buga wasanni takwas zuwa yanzu, inda ta samu nasara sau biyu, ta tashi wasa biyu, sannan ta sha kashi a wasanni hudu, abin da hukumar ta bayyana a matsayin rashin cika tsammanin magoya baya da shugabanni.
Don ci gaba da gudanar da horo, tsohon kyaftin na ƙungiyar kuma mataimakin koci, Gambo Muhammad, tare da kocin masu tsaron raga, Suleiman Shuaibu, za su jagoranci aikin horarwa na wucin gadi.
Haka kuma, kocin ƙungiyar matasa ta Junior Pillars, Garzali Muhammad, zai shiga cikin tawagar a matsayin mai taimako na ɗan lokaci.
Hukumar ta nuna godiya ga magoya bayan ƙungiyar saboda goyon bayansu duk da halin da ake ciki, tare da tabbatar musu cewa ana ɗaukar matakan da suka dace don dawo da nasarar ƙungiyar a gasar.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa ƙungiyar Kano Pillars ta ci tarar Naira miliyan 9.5 daga hukumar NPFL, tare da rage mata maki uku da ƙwallaye uku, saboda tashin hankali da magoya bayanta suka haifar a wasansu da Shooting Stars a baya-bayan nan.
Har ila yau, za ta buga wasanninta goma na gida a birnin Katsina ba tare da magoya baya ba.
A karon wasanta na tara, Kano Pillars ta sha kashi 2–1 hannun Barau FC a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.
Rabiu Ali ne ya fara zura ƙwallo a minti na 20, sai kuma Barau FC ta farke ta hannun Ibrahim Yahaya daga bugun fenariti, kafin Stanley Okafor Oganbor ya ci ta biyu a minti na 75.
Sakamakon wannan rashin nasara da hukuncin da aka ɗora kan ƙungiyar ya ƙara matsa wa jami’an fasaha da shugabanci na Kano Pillars lamba, yayin da ƙungiyar ke ci gaba da jan ƙafafunta a gasar, inda yanzu take a matsayi na 20 a jadawalin NPFL.













































