Hukumar kula da Ilimin Fasaha ta Kasa (NBTE) ta bayyana shirinta na gudanar da taron kasa da kasa karo na uku kan “ Tsarin Linux, da Koyon Na’ura” da kuma “Binciken Hada-hadar Kimiyya, Fasaha, Injiniya da Lissafi (STEM)” a watan Nuwamba 2025 a cibiyar UBEC da ke birnin Abuja.
A cikin sanarwar da shugaban sashen yada labarai na hukumar, Hajiya Fatima Abubakar, ta fitar a Kaduna, ta ce taron na da nufin sabunta tsarin Ilimin Fasaha da Koyon Sana’a (TVET) a fadin ƙasar nan da kuma karfafa matsayin Najeriya a harkar sabuwar fasahar (Artificial Intelligence) a duniya.
Ta bayyana cewa wannan taron na nuni da ci gaba a hadin gwiwar da NBTE ke yi da Kamfanin MOC-LLC ta Amurka, wanda aka kafa tun shekarar 2024 domin inganta basira da kwarewa a fannin koyon na’ura, Linux da fasaha tsakanin malamai a kwalejojin kimiyya da fasaha a Najeriya.
Hadin gwiwar ya sanya kwalejojin kimiyya da fasaha a Najeriya cikin sahun gaba wajen kirkire-kirkire, bincike, da sauyin fasaha a nahiyar Afirka.
Wannan kuma zai ba malamai da dalibai damar samun kwarewar aiki da kasuwanci a cikin sabon tsarin tattalin arzikin zamani.
A cewar Hajiya Abubakar, hukumar ta ƙaddamar da shirin horarwa mai taken “Kwarewa Bayan Takardar Shaida”, domin karfafa ilimin STEM da kirkire-kirkire, sana’o’i da amfani da tsarin Linux wajen warware matsalolin fasaha.
Sakataren zartarwa na NBTE, Farfesa Idris Bugaje, ya ce hadin gwiwar da hukumar ke yi da MOC-LLC na Amurka zai kara wa Najeriya ƙwarewa a fannin bincike da kirkire-kirkire, tare da fatan sakamakon binciken da za a gabatar a taron Nuwamba 2025 zai zama ainihin ayyukan da za su samar da ayyukan yi da bunkasa kasuwanci nan da 2026.
Bugu da ƙari, makarantar kimiyya da fasaha ta Kambolcha daga ƙasar Habasha ta shiga cikin shirin, alamar karuwar haɗin kan ƙasashen Afirka wajen ci gaban ilimin fasaha da bincike.
Malam Dr Ayalew Talema na Jami’ar Wollo ya jaddada bukatar haɗin kai tsakanin Najeriya da Habasha domin bawa matasan Afirka damar koyon fasahar koyon na’ura da fasahar zamani.
A yayin taron na watan Nuwamba mai zuwa, malamai da aka horas za su gabatar da takardun bincike kan amfani da Linux wajen koyon na’ura da fasahar zamani.
Wannan hadin gwiwar tsakanin NBTE da MOC-LLC na Amurka na nuna sabon babi a tarihin ilimin fasaha a Afirka, tare da tabbatar da kudirin Farfesa Bugaje na gina fasahar cikin gida, kirkire-kirkiren dorewa da samar da ayyukan yi ta hanyar bincike mai amfani.













































