Majalisar wakilan Najeriya zata gana da Buhari a sati mai zuwa don kowa karshen yajin aikin ASUU-Femi Gbajabiamil

WhatsApp Image 2022 09 29 at 11.27.37 AM 1 750x430 2
WhatsApp Image 2022 09 29 at 11.27.37 AM 1 750x430 2

Shugaban majalisar wakilan  Najeriya Femi Gbajabiamil, a ranar Alhamis yace shugabancin majalisar zai gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari, don kawo karshen tirka tirkar data ke faruwa tsakanin gwamnatin ta tarayya da kuma kungiyar malam jami’oi’ ta kasa ASUU.

Hakan na zuwa ne bayan ofishin babban akanta na kasa ya bayyana cewa a shirye yake da yai duba tare da gyra ga duk wata matsla data ke tattare da tsarin biyan albashi na (IPPIS) da kuma tsarin (UTAS), wanda yazamo babban jigon matsalar ASUU da gwamnatin tarayya.

Shugaban majalisar wakilan yace shugabanacin majalisar nan da kwanaki kadan zai tattara bayanai tattaunawar da sukai da masu ruwa da tsaki kan hanyoyin da za’a kawo karshen yajin aikin, ta yacce idon sun gana da shugaban kasa zasu mikamasa rahoton don yasamu damar yin nazari akai.

Yayin da yake jawabi a wajan taron da akai tsakanin shugabancin majalisar da masu ruwa da tsaaki, ya ce tattaunawar da kuma shawarawari da aka tattara yayin taron zai taimaka mutika don kawo karshen yajin aikin ASUU.

Jaridar Solacebasehausa ta rawaitu cewa wadan da suka hallarci taron sun hada da babban sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha; Chris Ngige; Folashade Yemi-Esan; AGF Mista Sylva Okolieaboh; Ben Akabueze; Kashifu Inuwa; Ekpo Nta da kuma shugaban kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, da sauransu.

Shugaban majalisar wakilan ya kuma tabbatarwa da kungiyar ta ASUU cewa da zarar sun gama ganawa da Buhari, zai gayyace su domin su tattauna abin da sukai da Buhari.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here